ĆŠalibai sun yi gagarumar zanga-zanga saboda satar dalibai a Lafia

Daliban Jami’ar Tarayya Lafia (Fulafia) sun fito kan tituna suna nuna rashin amincewa da ci gaba da yin garkuwa da ’yan’uwan da ake yi.

Idan ba a manta na, masu garkuwa da mutane sun kaddamar da wani hari a wani wurin da ke kusa da harabar Gandu, da ke kusa da Fulafia, kuma har yanzu ba a tantance adadin daliban da aka yi awon-gaba da su ba.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba.

Majiyoyi sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun afka wa gidan da ke wajen harabar makaranta, inda suka kama wasu daliba.

Da suke nuna bacin ransu da damuwarsu kan rashin tsaro da ke kara ta’azzara, daliban Fulafia sun fito kan tituna a ranar Alhamis, suna rike da alluna masu dauke da rubuce-rubuce daban-daban kamar, ‘Student Lives Matter’, da sauransu, da kuma nemam sakin takwarorinsu da aka yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba, wadanda a halin yanzu ba a san inda suke ba.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Wasu É—aliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karÉ“ar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...