Rundunar ‘Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar wuta tare da kama wasu hudu a yankin Jahi na babban birnin kasa.
Haka kuma, an kama ‘yan fashi na kwace motoci fiye da biyar kuma an kwato motoci 13 da aka sata yayin ayyukan da rundunar Scorpion ta FCT ta gudanar.
Yayin da aka gabatar da wadanda ake zargi a ranar Laraba a Abuja, Kwamishinan ‘Yan Sanda na FCT, Tunji Disu, ya bayyana cewa ‘yan fashin sun fara harbi a ranar 21 ga Oktoba bayan ganin jami’an ‘yan sanda da suka samu kiran neman dauki kan wani al’amari na fashi a yankin Jahi na FCT.
A cewarsa, yayin musayar wutar, ‘yan sanda sun kashe wasu daga cikin ‘yan fashin guda biyu, sun kwato wasu motoci biyu daga gare su, sannan suka kama wasu mutum biyu da aka bayyana sunayensu da Haruna Abdullahi, mai shekaru 32 daga karamar hukumar Ikara a jihar Kaduna, da Yerima Usman, mai shekaru 28 daga karamar hukumar Itoro a jihar Bauchi.
Ya ce, “Da zarar suka hangi motar sintirin ‘yan sanda, wadanda ake zargin suka bude wuta, wanda ya jawo musayar wuta har aka kashe wasu daga cikinsu biyu.”
Disu ya kara da cewa bayan wani binciken da aka sake yi a ranar 23 ga Oktoba, wadanda ake zargin sun kai ‘yan sanda kama wasu ‘yan kungiyar biyu: Abba Ismail, wanda aka fi sani da Dan-Abba, da Ashiru Suleiman, wadanda suka tsere daga wajen lamarin.
“Yayin bincike, wadanda ake zargin sun amsa cewa suna cikin wata kungiyar ‘yan fashi da makami karkashin jagorancin wani Dan Auwalu, wanda har yanzu yana tsere. Har zuwa yanzu, sun yi fashi da makami a yankunan Mabushi, Jahi, da Gishiri. A halin yanzu ana ci gaba da kokarin kama sauran mambobin kungiyar,” in ji shi.
Disu ya kuma bayyana sunayen wasu daga cikin ‘yan fashin motoci da aka kama sun hada da Arji Thomas, mai shekaru 32 daga karamar hukumar Gwoza a jihar Borno; Amobi Ndukwe, mai shekaru 40 daga karamar hukumar Awgu a jihar Enugu; da Amaechi Sampson, mai shekaru 26 daga jihar Imo.
Ya ce, su Thomas, Ndukwe, da Sampson sun kasance mambobin wata babbar kungiyar kwace motoci karkashin jagorancin wani Chidiebere, wanda har yanzu yana tsere.
A cewarsa, an kama wadanda ake zargin yayin da suke kokarin sayar da wata motar Toyota Corolla mai lamba KTW 2155D da aka sace.
“Yana da mahimmanci a lura cewa duka Arji Thomas da Amobi Ndukwe sun taba zama fursunoni. Yayin bincike, sun amsa cewa sun dade suna aikata sata a yankin Garki fiye da shekara daya da rabi, sun dauki alhakin satar motoci da dama a cikin birnin,” in ji Disu.
Yayin bayanin yadda aka kama Abang, Disu ya ce wani Philemon Olaoluwa ya kai rahoto a ofishin ‘yan sanda na tsakiya cewa mashininsa na Apo Mechanic Village, wanda aka bayyana sunansa da Abdulhamid Saidu, ya tsere da motarsa, wata Honda Accord mai launin toka shekara ta 2006 mai lamba RBC 40 bayan gyaranta ya dauke ta zuwa Jos.
Ya kara da cewa mashinin, wanda har yanzu yana tsere, ya bai wa Abang motar, wanda ya amsa cewa yana cikin wata kungiyar satar motoci dake aiki a Abuja, Filato da Nasarawa.