Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama Ibrahim Aliu mai shekaru 41 a duniya a Papa Olosun, Oja Odan a karamar hukumar Yewa ta Arewa bisa zarginsa da lalata da ‘yarsa mai shekaru 12 (an sakaya sunanta).
An kama Aliu ne a ranar Alhamis bayan matarsa, Temitope Egbebi, ta kai kara ofishin ‘yan sanda na Oja Odan.
Egbebi ta yi zargin cewa Aliu yana lalata da yarinyar a duk lokacin da ta ziyarce shi a lokacin hutu.
Ta shaida wa ’yan sanda cewa ta gano hakan ne bayan kai yarinyar zuwa Asibitin Jihar da ke Ilaro domin a duba lafiyarta da kuma jinyar yadda wani ruwa ke fita daga al’aurarta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Omolola Odutola, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.