Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da jabun takaddun shaida.

Mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda mai kula da shiyyar, Olatoye Durosinmi, ya tabbatar da kamen a ranar Talata yayin da yake gabatar da wanda ake zargin a gaban manema labarai a Legas.

Durosinmi ya ce jami’an sashen yaki da satar fasaha na shiyyar sun kama wanda ake zargin, wanda ya yi ikirarin cewa shi ne Manajan Daraktan Cibiyar Kiwon Lafiya ta Skylink a Ikorodu.

“Bisa bayanan sirrin da rundunar ta samu ta hannun ‘yan kabilar Elepe game da ayyukan wanda ake zargin, wata tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin SP Mariam Ogunmolasuyi, ta kai dauki.” Inji shi.

More from this stream

Recomended