Ƴansanda sun gurfanar da mutumin da ya yi lalata da ɗiyarsa

A ranar Alhamis ne rundunar ‘yan sandan shiyya ta 6 da ke Kuros Riba ta gurfanar da Adamu Ibrahim Umaru mai shekaru 48 a duniya bisa zargin yin lalata da ‘yarsa mai shekaru 15 da haihuwa.

Mai magana da yawun shiyya ta 6, Nelson Okpabi, ya shaidawa manema labarai cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Juma’a, 15 ga watan Nuwamba, bisa wata kara da wata uwargidan mai suna Aisha ta shigar.

“Ma’aikatan sashen kare hakkin bil’adama na shiyyar da aka shigar musu da kara a gaban ƴansandan domin gudanar da bincike, a ranar 15 ga Nuwamba, 2024 sun kama Malam Adamu Ibrahim Umaru.

“Wanda ake zargin dan asalin karamar hukumar Bundugudu ne ta jihar Zamfara, yana zaune a lamba 27 Edem Odo Street, Calabar wanda ya lalata ‘yarsa ba bisa ka’ida ba,” inji shi.

Kakakin ya ce, mai shigar da kara ta bayyana cewa ta lura da canje-canje a cikin halittar yarinyar kuma ta kai ta asibiti inda gwajin da aka yi mata ya tabbatar da cewa tana da ciki na mako tara.

Rundunar ‘yan sandan ta ce yarinyar a cikin bayaninta, ta yi zargin cewa mahaifinta ne ke da alhakin cikin.

Ta kara da cewa mahaifinta ya fara lalata da ita ne a shekarar 2023 a wani otel da ke Calabar kuma ya yi mata barazanar cewa zai kashe ta idan ta bayyana hakan ga kowa.

More from this stream

Recomended