Ƴansanda a Katsina sun yi nasarar cafke wasu tantiran masu safarar alburusai wa ƴanbindiga

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’a ta sanar da cewa ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda uku tare da kwato manyan harsasai masu yawa a cikin garin Dutsinma da ke jihar. 

Kamen nasu, a cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Sadiq, na daga cikin gagarumin nasarar da ta samu a yaki da ‘yan fashi da makami.

Wadanda ake zargin su ne Ahmed Mohammed Kabir, mai shekaru 25, mazaunin Hayin Danmani, jihar Kaduna; Mannir Musa, mai shekaru 25, daga garin Dutsinma, karamar hukumar Dutsinma da Aliyu Iliya, mai shekaru 25, daga kauyen Dankauye ta hanyar Ummadau, karamar hukumar Safana, jihar Katsina.

An kama su ne a ranar 29 ga watan Agustan 2024, da misalin karfe 1245, yayin da suke kokarin kai harsashi dari bakwai da arba’in (740) ga wasu ‘yan bindiga ne a dajin Yauni, kauyen Ummadau, cikin karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, a cewar hukumar  ‘yan sanda.

More from this stream

Recomended