Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a coci-coci a Bakinpah-Maro da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna ranar Lahadi. 

Tsohon shugaban karamar hukumar Kajuru, Cafra Caino, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa maharan sun isa wajen da yawansu da misalin karfe 10 na safe.

An ce sun kai hari kan cocin ECWA da cocin Katolika.  

“‘Yan fashin sun zo da yawa kuma suka kai hari kan majami’u biyu,” in ji Caino, a cewar jaridar The Nation.

Daga cikin wadanda aka sace har da Bernard Gajera, wani Fasto daga daya daga cikin cocin.

Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan ba ta fitar da sanarwa kan harin ba.

Wannan harin dai ya zo ne a daidai lokacin da al’ummar Maro ke kokarin samar da kudade a wani ofishin tsaro domin jawo hankalin jami’an tsaro da dama, tare da magance matsalolin tsaro da ke ci gaba da dakile ayyukan noma.

More from this stream

Recomended