Ƴan sanda sun sha alwashin ceto ɗaliban jami’a da aka yi garkuwa da su a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Larabar da ta gabata, ta ce tana kan gaba a halin da ake ciki dangane da sace dalibai mata biyar na Jami’ar Tarayya Dutsinma, jihar Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Sadiq, ne ya bayyana hakan a cikin wata ‘yar gajeruwar sanarwa a ranar Laraba, inda ya ce rundunar ta tura kayan aiki da nufin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su, tare da kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki yayin da ake ci gaba da bincike.

“A ranar 4 ga Oktoba, 2023, da misalin karfe 2 na safe, wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun yi garkuwa da wasu dalibai mata biyar na jami’ar tarayya ta Dutsinma.

“Rundunar ta na kan gaba wajen lamarin, domin ta yi amfani da duk wata dabarar aiki da nufin ceto wadanda abin ya shafa.”

More News

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Majalisar dokokin Zamfara ta tsige kakakinta saboda tsanantar rashin tsaro a jihar

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige kakakinta, Bilyaminu Moriki, tare da nada Bashar Gummi, a matsayin kakakin majalisar. Hakan ya biyo bayan kudirin da dan...

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kisan mutane shida da wasu ‘yan bindiga suka yi a karamar hukumar Faskari a jihar. Jami’in hulda...

Sace-sacen motoci ya yawaita a Adamawa—Ƴan sanda

Ana ci gaba da samun karuwar sace-sacen motoci a jihar Adamawa, kamar yadda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar. Rundunar ‘yan sandan ta bayyana haka...