Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar.

A wata sanarwa ranar Litinin mai magana da yawun rundunar,Mansur Hassan ya ce mutanen biyu da ake zargi an kama su ne ranar 4 ga watan Afrilu biyo bayan ƙwararan bayanan sirri da aka tattara akan su.

Alkali Danladi mai shekaru 45 da kuma Gayya Koddi mai shekaru 40 su ne mutanen da aka kama.

Hassan ya ce ƴan sandan sun daɗe suna fakon  Danladi kan samarwa da ƴan fashin daji makamai inda a ƙarshe aka kama shi a ƙauyen Tsurutawa dake kan hanyar Kaduna zuwa Jos.

Ya ce an kama Danladi da makamai da dama da aka haramta amfani da su.

Ya ce faɗaɗa binciken da aka yi ne ya kai ga kama Koddi a yayin da ake cigaba da neman wasu mutane biyu.

Danladi na kan hanyarsa ta dawowa daga Jos lokacin da aka kama shi.

More from this stream

Recomended