Ƴan sanda sun kama matar da ta cakawa yarinya ƴar shekara 8 wuƙa a Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce jami’anta sun samu nasarar kama matar da ta cakawa yarinya yar shekara 8 wuka a ciki.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne ya bayyana haka.

A wani fefan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook matar ta bayyana dalilinta na aikata wannan ɗanyen aiki.

Lamarin ya faru ne a unguwar Kureƙen Sani dake ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar.

Matar da aka kama mai suna Fatima ta bayyana cewa tana zaune ne a unguwar Gadon Kaya dake cikin birnin Kano inda anan ta ɗauki yarinya ta tafi da ita zuwa inda ta aikata laifin.

Ta fadawa kakakin rundunar cewa ta aikata haka ne saboda tana zargin mahaifin yarinyar yana bawa mijin ta shawarar ya ƙara aure.

A makon da ya gabata ne aka ga yarinyar mai suna Sharifa Usman da wuka soke a cikin ta tana yawo inda aka kaita Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano kuma likitoci suka yi mata aiki.

More from this stream

Recomended