A cigaba da yaƙi da ƴan fashin daji, ɓatagari da kuma rashin tsaro a fadin Najeriya jami’an rundunar ƴan sandan jihar Sokoto sun samu nasarar kama wasu mutane biyar da ake zargin su da yin garkuwa da mutane akan hanyar Bodinga- Tambuwal.
Mutanen biyar sun faɗa hannun jami’an tsaro ne a ranar 13 ga watan Faburairu da misalin ƙarfe 08:30 na dare sakamakon bayanan sirri da rundunar ƴan sandan ta samu.
An kama mutanen ɗauke da bindigar AK-47 guda uku da kuma harsashi guda 90.
Mutanen da aka kama sun haɗa da Abdullahi Ali,Aliyu Muhammad Abdullahi Umar, Aliyu Abdullahi da kuma Mohammed Anas dukkaninsu sun amsa cewa suna kan hanyarsu ta zuwa Tambuwal ne domin yin garkuwa da mutane kafin su fada komar jami’an ƴan sandan.