Ƴan sanda sun ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su a Katsina

Mutane huɗu da aka yi garkuwa da su jami’an yan sanda suka ceto a karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina.

Abubakar Sadiq-Aliyu mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce an ceto su ne a ranar Asabar da haɗin gwiwar jami’an sojoji.

Aliyu ya ce an samu nasarar ceto mutanen ne a lokacin da jami’an tsaro suke gudanar aikin sintiri da suka saba a wajen ƙauyen Dankolo.

” A kokarin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a yan sanda da haɗin gwiwar jami’an soja sun ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban a jihar” ya ce.

Ya kara da cewa likitoci sun duba mutanen kuma tuni aka haɗa su da iyalansu.

More News

Ɗan ta’addar Boko Haram ya miƙa kansa ga sojoji

Alhaji Wosai wani mamba a ƙungiyar ƴan ta'addar Boko Haram ya miƙa kansa ga dakarun sojan Najeriya na rundunar Operation Haɗin Kai. Rahotanni sun bayyana...

An kuɓutar da wasu ɗaliban da aka sace a jami’a a Kogi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta bayyana cewa an ceto 14 daga cikin daliban jami’ar kimiyya da fasaha ta Confluence da ke Osara Okene...

Hukumar NMDPRA ta rufe wani gidan mai da ya karkatar da tankar man fetur 18

Hukumar NMDPRA dake lura da tacewa tare rarraba man fetur da iskar gas ta rufe gidan man Botoson Oil and Gas LTD dake jihar...

Jirgin saman kamfanin Xejet ya zame daga kan titin filin jirgin saman Lagos

A ranar Asabar ne wani jirgin sama mallakin kamfanin Xejet ya zame daga kan titin filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos. Hukumar NSIB dake...