Ƴan sanda sun ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su a Katsina

Mutane huɗu da aka yi garkuwa da su jami’an yan sanda suka ceto a karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina.

Abubakar Sadiq-Aliyu mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce an ceto su ne a ranar Asabar da haɗin gwiwar jami’an sojoji.

Aliyu ya ce an samu nasarar ceto mutanen ne a lokacin da jami’an tsaro suke gudanar aikin sintiri da suka saba a wajen ƙauyen Dankolo.

” A kokarin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a yan sanda da haɗin gwiwar jami’an soja sun ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban a jihar” ya ce.

Ya kara da cewa likitoci sun duba mutanen kuma tuni aka haɗa su da iyalansu.

More from this stream

Recomended