Ƴan sanda a Kaduna sun kama mai garkuwa da mutane bayan da suka ƙi karɓar cin hancin naira miliyan 1

Rundunar yan sandan jihar Kaduna, ta ce jami’anta sun samu nasarar kama wani mai suna Bello Muhammad da ake zarginsa da yin garkuwa da mutane a jihar.

A wata sanarwa ranar Alhamis, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Mansur Hassan ya ce wanda ake zargin yana jagorantar gungun wasu masu garkuwa da mutane da suka addabi al’ummar jihar.

Hassan ya ce Muhammad wanda ɗan asalin jihar Zamfara ne an kama shi ne lokacin da jami’an yan sanda dake aiki da ofishin yan sanda na garin Tafa suka kai farmaki wani hotel dake garin Tafa na jihar.

Ya ce wanda ake zargin dake da shekaru 28 ya yiwa ƴan sanda tayin toshiyar baki ta naira miliyan ɗaya amma suka ƙi karɓa.

Ya ce jami’an ƴan sandan sun gano naira miliyan 2, 350,000 da suke kyautata zaton wani bangare ne na kudin fansa..

Sanarwar ta kara da cewa binciken da aka gudanar a cikin wayarsa an samu hoton sa yana riƙe da bindiga ƙirar Ak-47 a wani daji.

More from this stream

Recomended