Jami’an Kenya sun kama akalla ’yan Najeriya uku a Mwaliko Estate da ke Mwea Town bisa zargin wata makarkashiyar zamba ta yanar gizo.
Rahoton Tuko News ya nuna cewa rundunar Directorate of Criminal Investigations (DCI) ta cafke mutanen ne a ranar Laraba, bayan samun korafe-korafe daga mazauna unguwar game da abin da suka bayyana a matsayin mu’amalar dare wadda akwai tuhuma a ciki.
An bayyana sunayen wadanda aka kama a matsayin Peter Chukwujekwu, Alazor Chukulute Sunday, da Nnalue Chiagozie Samwe.
A cewar rahoton da aka fitar a ranar Alhamis, jami’an tsaro sun fatattake su daga cikin gidansu bayan alamu sun nuna akwai ayyukan da ba su dace ba da suke faruwa a wurin.
Rahoton ya ce mutanen sun yi ikirarin gudanar da kasuwancin yanar gizo, amma suna zaune a Kenya ba bisa ka’ida ba tare da samun lasisin aiki ba.
Ƴan Najeriya Uku Sun Shiga Hannun Jami’an Kenya Kan Zargin Zamba

