Ƴan mata 15 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Sokoto

Ƴan mata 15 aka rawaito sun mutu a wani hatsarin jirgin kwale-kwale da ya faru a ƙauyen Ɗandeji dake karamar hukumar Shagari ta jihar Sokoto.

Ƴan matan na kan hanyarsu ne ta zuwa ɗebo itace a wani daji dake kusa lokacin da jirgin ya kife da su ranar Talata da safe.

A cewar wani shedar gani da ido jirgin na dauke da ƴan mata sama da 40 lokacin da lamarin ya faru.

Wani mazaunin yankin, Muhammad Ibrahim ya ce tuni aka samu gawarwaki 15 kuma masu iyo na cigaba da lalubo ragowar mutane.

Shugaban karamar hukumar, Shagari, Aliyu Abubakar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ana yiwa gawarwakin sutura domin a yi musu jana’iza

More News

Wani sojan ruwan Najeriya ya hallaka abokin aikinsa a Zamfara

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta kama wani sojan ruwa mai suna A. Akila bisa zarginsa da kashe abokin aikinsa.An tura Akila zuwa sansanin Forward Operating...

Kotu ta bada umarnin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Wata babbar kotu a jihar Kano ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar wato KANSIEC da ta cigaba da shirye-shiryen gudanar da...

Kotu ta bada umarnin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Wata babbar kotu a jihar Kano ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar wato KANSIEC da ta cigaba da shirye-shiryen gudanar da...

Ministan tsaro Badaru ya yaba wa gwamnan Zamfara saboda tallafa wa aikin soji a jihar

Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya jinjina wa Gwamna Dauda Lawal bisa jajircewarsa da ci gaba da tallafa wa ayyukan soji a Jihar Zamfara.Ministan...