Ƴan KAROTA sun kama jabun magungunan da darajarsu ta kai naira miliyan 50

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano, KAROTA, ta kama wasu jabun magungunan da kudinsu ya kai Naira miliyan 50 a Kano.

Kakakin hukumar, Nabilusi Abubakar, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kano.

Ya ce, “Mota mai lamba MMR 153 XA dauke da magungunan jabu an kama ta ne a daren Juma’a da misalin karfe 9:00 na dare a hanyar Murtala Muhammed.

“Wasu daga cikin ma’aikatan sun ce suna zargin direban na dauke da muggan kwayoyi.

“Nan da nan direban ya ga ma’aikatan, sai ya gudu wanda hakan ya sa suka binciki motar.

“Magungunan da ake zargin na jabu sune maganin kashe zafi (masu kashe zafi), maganin tari da kuma maganin zazzabin cizon sauro.”

Ya bayyana cewa Manajan Daraktan KAROTA, Faisal Kabir ya ce hukumar ba za ta bari a shigo da miyagun kwayoyi cikin jihar ba.

Mista Kabir ya yi kira ga jama’a da su daina siyan magunguna daga hannun ƴan talla da kuma wadanda ba su yi rajista ba domin kauce wa illar hakan.

More News

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...