Ƴan bindiga sun shiga wata unguwa a Abuja

Kimanin watanni takwas ke nan da masu garkuwa da mutane suka kai hari Estate Grow Homes, kusa da Kuchibiyi a Unguwar Kubwa a babban birnin tarayya Abuja, suka yi awon gaba da mutane akalla tara.

Yanzu ma sun sake dawow ranar Alhamis da daddare suka kama mutane uku.

Wadanda abin ya shafa – ma’aurata da wani mutum, an yi garkuwa da su ne daga wasu gidaje guda biyu a cikin unguwar.

Alamu sun nuna azauna yankin suna cikin fargaba.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar, sun tsere ne ta hanyar daji.

Wata majiyar tsaro a gidan da ta dage a sakaya sunanta saboda ba shi da izinin yin magana da manema labarai ta ce bayan da suka kai farmaki yankin da misalin karfe tara na dare, ‘yan bindigar sun yi harbin iska don tsorata mutane.

Hat yanzu dai ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane suna cin karensu ba banbbaka a yankunan arewacin Najeriya.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Wasu ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karɓar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...