Ƴan Bindiga Sun Sace Mutum 5 Ba Bayan Sun Harbe Likita a Asibitin Kankara

Daga Sabiu Abdullahi

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun kai hari a Asibitin Kankara da ke Karamar Hukumar Kankara a Jihar Katsina, inda suka harbe wani likita kuma suka yi garkuwa da ma’aikatan asibiti biyar.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSP Abubakar Aliyu, ya fitar.

DSP Aliyu ya bayyana cewa wadanda suka ji rauni suna samun kulawar likitoci, sannan ’yan sanda na ci gaba da farautar masu laifin domin cafke su da kuma ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin.

“A ranar 14 ga Janairu, 2025, da misalin karfe 8:20 na dare, wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai kamar bindigogin AK-47, suka kai hari kan Asibitin Kankara, suna ta harbe-harbe.

“Bayan samun rahoton, DPO na Kankara ya jagoranci tawagar ’yan sanda zuwa wurin domin dakile harin, inda aka yi musayar wuta da ’yan bindigar.

Ya kara da cewa Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Katsina, Aliyu Abubakar Musa, ya yi Allah-wadai da harin da aka kai kan ma’aikatan lafiya da cibiyoyin kiwon lafiya.

More from this stream

Recomended