
Ƴan mata shida dake da shekaru 15 zuwa 17 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun yi garkuwa da su a garin Pandogari dake ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Mazauna gari sun faɗawa jaridar Daily Trust cewa ƴan fashin dajin sun farma garin da tsakar daren ranar Laraba inda suka kashe wani ɗan bijilante Aliyu Aminu tare da yin garkuwa da ƴan matan..
Ƴan fashin dajin masu yawa sun shiga garin ne daga wajejen ɓangaren Birnin Gwari ta wajen Kwalejin Fasaha ta Mamman Kantagora dake Pandogari.
Wata majiya ta bayyana cewa ƴan matan da aka yi garkuwa da su an ɗauke su zuwa Dajin Kwangel.
Ɗaya daga cikin majiyar ta bayyana cewa ƴan fashin dajin sun riƙa bi gida-gida a lokacin harin.
Shugaban ƙaramar hukumar Rafi, Ayuba Usman Katako ya tabbatar ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da ya yi da gidan rediyon Prestige FM.