
Ƴan bindiga sun kashe Farfesa Emeka Chukwuma wani malami a jami’ar jihar Delta dake garin Abraka.
A cewar jaridar Punch, Farfesa Chukwuma mai shekaru 56 ya dawo gidansa dake Umueji a Asaba babban birnin jihar Delta ranar Juma’a domin yin hutun ƙarshen mako da ya saba yi amma a wannan karon sai ƴan bindiga suka bindige shi har lahira.
“An kashe Prof Emeka Chukwuma ranar Juma’a da daddare a Asaba malami ne a jami’ar jihar Delta dake Abraka, ” a cewar wata majiya da ta gana da jaridar ta Punch.
“Prof Chukwuma ya saba zuwa gida a duk ƙarshen mako. Amma cikin rashin sa’a ya dawo jiya hutunsa na ƙarshen mako amma sai aka kashe shi a gidansa.”
” A yanzu da nake magana da kai babu tsaro a Asaba. Mun shiga ruɗu kan halin da ake ciki.”
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Bright Edafe bai ce komai ba da aka nemi jin ta bakinsa.