Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CBS ta bada rahoto.
Wani jami’in ma’aikatar wajen Amurka ya faɗawa kafar yaɗa labaran cewa Kurt Campbell mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka da kuma Ali Lamine Zeine firaministan ƙasar Nijar sun yi wata ganawa ranar Juma’a a birnin Yamai kan yadda za a shirya ficewar dakarun cikin tsari daga Nijar.
Jami’an biyu sun jaddada muhimmancin dangantaka a tsakanin ƙasashen biyu inda suka amince su cigaba da haɗa kai a fannin da ɓukatar su tazo ɗaya.
Ƙasar ta Amurka ta amince ta rufe sansanin sojanta dake garin Agadez inda anan ne ta girke jiragen yaƙinta marasa matuƙi.
Kusan sojan Amurka 1000 ne ke zaune ƙasar ta Nijar inda suke yaƙi da ƙungiyoyin ƴan ta’adda dake yankin Sahel.