Ekene Abubakar Adams ɗan majalisar wakilai dake wakiltar ƙananan hukumomin Chikun/Kajuru a majalisar wakilai ta tarayya ya mutu.
A cikin wata sanarwa da Akin Rotimi Jr mai magana da yawun majalisar ya fitar ya ce Adams ya mutu da tsakar daren ranar Talata yana da shekaru 39 a duniya.
Sanarwar ta ce “Majalisar wakilai na alhinin sanar da mutuwar mamba a majalisar wakilai ta 10, Ekene Abubakar Adams( LP Kaduna) wanda ya mutu da tsakar daren ranar Talata yana da shekaru 39.”
Sanarwar ta cigaba da cewa wakili Adams mai’ aikacin gwamnati ne mai sadaukarwa dake da sha’awar jagoranci harkokin wasanni da kuma tallafawa mararsa ƙarfi.
Kafin rasuwar ɗan majalisar ya kasance shugaban kwamitin wasanni na majalisar.