Ɗan majalisar jiha ya mutu bayan kwana uku da fara aiki

Garba Madami, mamba a majalisar dokokin jihar Kaduna ya mutu.

Madami dan jam’iyar PDP na wakiltar mazabar Chikun a majalisar ya mutu a wani asibiti dake Kaduna.

Ba’asan musabbabin mutuwarsa ba.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, David Madami ɗa ga marigayin ya ce mutuwar mahaifin nasa ta kaɗa shi sosai.

Marigayin ya kasance tsohon kwamishina kasafin kudi da tsare-tsare ya kuma taɓa rike muƙamin mashawarci kan harkokin siyasa ga tsohon gwamnan Kaduna, Patrick Ibrahim Yakowa.

Mutuwar ta sa na zuwa ne kwana uku bayan da aka rantsar da su a matsayin yan majalisa.

More from this stream

Recomended