Ɗan Ƙunar Baƙin Wake Ya Kashe Kansa A Kaduna

Wani mutum da ake zargin dan kunar baƙin wake ne a kungiyar Boko Haram ya tarwatsa kansa da bom a gidansa dake kan titin Ibrahim Haske a unguwar Keke dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Mutumin ya tashi bom ɗin ne domin gudun kada jami’an tsaro su kama shi.

Wasu majiyoyi dake unguwar sun ce jami’an tsaro sun dade suna sanya ido akan mutumin kafin daga bisani su bi sawunsa zuwa wani gida dake unguwar da ta Keke inda yake buya a ciki.

Wata majiyar ta bayyana cewa jami’an hukumar DSS, yan sanda da kuma sojoji su ne suka zagaye gidan inda suka riƙa musayar wuta bayan da ya fuskanci jami’an tsaron sun kusa cimmasa ɗan ta’addar ya tarwatsa kansa da bom.

An gano bindigar AK-47 tare da wasu bama-bamai biyu da basu fashe ba a gidan mutumin.

More News

An Jikkata Jami’an Tsaro A Harin Da Ƴan Bindiga Su ka Kai Wa Ayarin Motocin Yahaya Bello

A jikkata wasu jami'an tsaro a wani hari da yan bindiga su ka kai kan jerin ayarin motocin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ranar...

Bala Muhammad ya zama shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP

An zaɓi gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad a matsayin sabon shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP. Siminalayi Fabura zaɓaɓɓen gwamnan jihar Rivers shi ne mataimakin shugaban...

Za mu sake bitar mafi karancin albashi a Najeriya—Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin sake nazarin mafi karancin albashin ma’aikata domin dacewa da yanayin tattalin arzikin kasar nan. A cewarsa, akwai bukatar...

EFCC na zargin tsohuwar ministar mata a mulkin Buhari da karkatar da naira biliyan 2

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta titsiye tsohuwar ministar harkokin mata Pauline Tallen kan zargin azurta kai ta...