Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa sun cafke wata mata dauke da harsasai a cikin galan din mai a garin Keffi da ke karamar hukumar Keffi a jihar.
Matar mai suna Hauwa Sani, tare da wani yaro dan shekara biyu, an ce sun fito ne daga kauyen Doro da ke jihar Katsina.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Rahman Nansel, ya fitar a ranar Asabar a garin Lafia, ya ce matar ta dauko harsashin ne daga karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa amma an kama ta a hanyar ta ta komawa Katsina.
“A ranar 23/8/2024 da misalin karfe 1710 na safe, bisa samun sahihan bayanai, jami’an ‘yan sanda na sashen Keffi sun kama wata Hauwa Sani tare da wani yaro dan shekara 2 a kauyen Doro, jihar Katsina.
“Saboda haka, an kwato alburusai dari da ashirin da hudu (124) na Anti Aircraft da aka boye a cikin galan ɗin mai, wayar hannu ta Tecno daya, da kudi naira dubu saba’in da takwas da dari biyar (N78,500).”