Ƴan sandan jihar Adamawa sun kama wani magidanci mai suna Ibrahim Abubakar dan shekara 33 da haihuwa da ke zaune a unguwar Sabon Gari-Futy a karamar hukumar Girei da laifin daba wa matarsa Hajara Sa’adu ‘yar shekara 25 wuka har lahira.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka ba wa manema labarai a ranar Talata.
A cewar sanarwar, “Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a ranar 8 ga Afrilu, 2024, ta kama wani mutum mai shekaru 33 da laifin kashe matarsa Hajara Sa’adu mai shekaru 25 da haihuwa.
“An kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da mahaifin marigayiyar ya gabatar wa ‘yan sanda da kuma binciken farko da aka gudanar wanda ya kai ga gano bayanan kayan aiki a wurin da laifin ya faru wanda ke da alaka da shi.“
Yan sandan dai na ci gaba da gudanar da bincike kam lamarin.