Ƴansanda sun ƙaryata labarin garkuwa da jami’insu

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya yi watsi da jita-jita da ke yawo game da zargin sace wani jami’in ‘yan sanda na Legas.

A cikin wata sanarwa da aka wallafa  a shafin X a ranar Laraba, Hundein ya bayyana cewa DPOn da ake magana a kai yana cikin koshin lafiya a ofishinsa, yana gudanar da ayyukans don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi da ke karkashin ikonsa.

Ya nuna godiya ga wadanda suka nuna damuwa.

More from this stream

Recomended