Ƴan sanda sun sake rufe majalisar dokokin Plateau, a Jos babban birnin jihar.
Wannan lamarin dai ya haifar da zaman zullumi da neman tayar da tarzoma a harabar a yau Laraba.
Rahotanni sun nuna cewa wani dan majalisar, Gwottson Fom, daga mazabar Jos ta Kudu ya tabbatar da faruwar lamarin.
Dan majalisar wanda ya soki abin da ƴan sandan suka yi, ya ce matakin ya hana mambobin zamansu na yau Laraba.