Ƴan Sanda Sun Kama Wasu Mutane Biyu Da Ake Zargi Da Yiwa Yarinya Ƴar Shekara 13 Fyaɗe

Jami’an ƴan sanda na rundunar ƴan sandan jihar Gombe sun kama wasu mutane biyu  da ake zargi da yiwa wata yarinya ƴar shekara 13 fyaɗe a wata gona dake garin Bajoga a ƙaramar hukumar Funakaye ta jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar,ASP Mahid Abubakar shi ne ya bayyana haka lokacin da yake nuna mutanen a gaban ƴan jaridu a Gombe.

Abubakar ya bayyana Yayaji Muhammad mai shekaru 24 da kuma Muhammad Barau mai shekaru 20 a matsayin mutanen da aka kama ake kuma zarginsu da aikata laifin.

Ya ce an kama su ne biyo bayan korafi da wani mai suna Mallam Jauro mahaifin yarinyar ya shigar gaban rundunar.

More from this stream

Recomended