Rundunar ƴansandan jihar Filato ta kama wani matashi, Joseph Yakubu mai shekaru 29 da ake zargi da kisan mahaifinsa Yakubu Dalyop ta hanyar buga masa taɓarya.
Da yake gabatar da mai laifin a gaban ƴan jarida a hedkwatar rundunar ƴan sandan jihar Filato,kwamishinan ƴan sandan jihar Hassan Steve Yabanet ya ce lamarin ya faru bayan da mahaifin da ɗan nasa suka samu saɓani inda shi kuma ya ɗauki taɓarya ya buge shi a ka.
Ya ce lamarin da ya faru a ranar 15 ga watan Fabrairu a Kambel dake Anglo-Jos inda wani maƙocinsu ya kai rahoton faruwar haka ofishin ƴan sanda na Anglo-Jos a ranar 20 ga watan Faburairu bayan da mutumin ya mutu a asibitin kwararru na jihar Filato inda yake jiya.
Kwamishinan ya ce an ajiye gawar a ɗakin ajiye gawarwaki inda ya ce da zarar an kammala bincike za a tura mai laifin zuwa kotu.