Ƴan sanda sun kama mutane 4 masu garkuwa da mutane a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta ce jami’an tsaro sun kama wasu mutane huÉ—u da ake zargin Æ´an fashin daji ne dake addabar birnin.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, mai magana da yawun rundunar Æ´an sandan birnin, Josephine Adeh ta ce an kama mutanen ne a ranar 7 ga watan Yuni a yayin wani samamen haÉ—in gwiwa da ya haÉ—a da sojojin dake tsaron fadar shugaban, jami’an DSS, mafarauta da kuma Æ´an sanda.

Adeh ta ce jami’an tsaro sun yi amfani da bayanan sirri inda suka farma wasu sanannun sansanin masu garkuwa da mutane dake Gidan Dogon da kuma Dajin Kweti dake Kaduna kan iyaka da Abuja inda suka bi sawun mutanen suka kuma kama su.

Ta ce mutanen da aka kama sun haɗa da Yahaya Abubakar mai shekaru 25; Mohammed Mohamed, mai shekaru 32, wanda tsohon mai laifi ne ; Umar Aliyu, mai shekaru 20; da kuma  Nura Abdullahi mai shekaru 32 wanda shima tsohon mai laifi ne.

Mutanen sun amsa laifin kasancewa mambobi na Æ™ungiyar masu garkuwa da mutane da sukewa kansu laÆ™abi da ‘Mai One Million’ wanda su ne da alhakin garkuwa da mutane da dama Abuja da kewayenta.

More News

Muna aiki tukuru don kawar da aikata manyan laifuka a Najeriya—Tinubu ga Daraktan FBI

A ranar Juma’a ne shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncin daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI), Christopher Asher Wray, inda ya...

Sojojin sun kama wani mai safarar bindigogi a jihar Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin  samar da  tsaro a jihar Filato sun ka ma wani mai safarar  bindiga da ake nema ruwa...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya akan hanyar Abuja-Kaduna

Fasinjoji da dama ne aka bada rahoton an yi garkuwa da su bayan da ƴan fashin daji suka buɗe kan wata mota ƙirar bus...

Kotu ta yanke wa É—ansanda hukuncin kisa saboda laifin kisan kai

Wata babbar kotun jihar Delta dake zamanta a Asaba a ranar Talata ta yanke wa Sufeta Ubi Ebri na rundunar ‘yan sandan Najeriya hukuncin...