Ƴan sanda sun kama masu safarar makamai wa ƴan bindiga

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Karasuwa a jihar Yobe sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga makamai da alburusai.

An kama wadanda ake zargin ne da makamin roka.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim ya fitar.

A cewar PPRO mutanen biyu wadanda ake zargin, Hassan Abubakar mai shekaru 35, da Abubakar Shehu mai shekaru 32, dukkansu ‘yan kabilar Maradun ne a jihar Zamfara.

“An kama wanda ake zargin na farko, Hassan Abubakar ne a lokacin da yake tuka motar bas mai mutane 18 a Karasuwa a kan ƙoƙarinsa na karbar RPMG. An kama shi ne bayan ya tattara bindigar bam.

“Wanda ake zargin na farko ya amsa cewa wanda ake zargi na biyu, Abubakar Shehu, dan aike wa ‘yan fashi ne a jihar Zamfara, kuma jami’an ‘yan sanda daga jihar Yobe sun bi sawun su tare da kama su a Maradun,” in ji jami’in hulda da jama’a na ƴan sandan.

Ya kara da cewa wadanda ake zargin suna baiwa ‘yan bindiga bindigu ne a jihohin Zamfara, Kano, Niger, Zaria, Yobe da dai sauransu.

More News

Kotu ta sauke kakakin majalisar Nasarawa

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Rt. Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi dan jam’iyyar...

Masu cin gajiyar shirin Npower na kokawa game da rashin biyansu

Wasu masu cin gajiyar shirin gwamnatin tarayya na N-Power a ranar Litinin sun koka kan yadda ake ci gaba da biyan su alawus-alawus din...

Tinubu ya sake naɗa Mele Kyari a matsayin shugaban NNPCL

Shugaba Bola Tinubu ya sake nada Malam Mele Kyari a matsayin babban jami’in gudanarwa na kamfanin man fetur na kasa (NNPCL). An bayyana hakan ne...

Ba baƙon abu ba ne don an haifi yaro da haƙori a bakinsa—in ji masana lafiyar yara

Likitocin kula da lafiyar yara sun ce jariran da ke da hakora daya ko biyu a lokacin haihuwa hakan ba baƙon al'amari ba ne. Wannan...