Rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar jami’anta biyu a wata musayar wuta da aka yi da wasu ƴan bindiga a ƙauyen Natsini dake ƙaramar hukumar Argungu ta jihar.
A wata sanarwa ranar Asabar, Nafiu Abubakar mai magana da yawun rundunar ya ce ƴan bindigar da ake kyautata zaton ƴan ta’addar Lakurawa ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 1 :00 na dare “Sun farma gonar Alhaji Lawan Black da kuma wata rigar Fulani dake kusa a ƙauyen Natsini dake kan titin Argungu zuwa Kangiwa inda suka sace shanu da ba a san yawan su ba, ” a cewar sanarwar.
“Da samun faruwar rahoton tawagar jami’an tsaro dake tabbatar da tsaron manyan hanyoyi sun garzaya ya zuwa wurin suka riƙa musayar wuta da ƴan bindigar suka kaɗa su cikin daji wasunsu da raunin harbin bindiga suka kuma kwato wasu daga cikin shanun.”
“Abun takaici ƴan sanda biyu sun mutu a musayar wutar,”
Sanarwar ta ƙara da cewa kwamshinan ƴan sandan jihar, Bello M Sani ya ziyarci wurin da lamarin ya faru kana daga bisani ya kai ziyara fadar Sarkin Argungu, Alhaji Dr Sama’ila Muhammad Mera.