Ƴan sanda a Kano sun kama wani ɗan daba da ya kashe wani matashi

Jami’an ƴan sanda a jihar Kano, sun samu nasarar kama wani ɗan daba da ya kashe wani matashi a unguwar Dorayi dake birnin Kano.

Matashin mai suna Abba Garba wanda aka fi sani da Ɗan Ƙuda dake zaune a unguwar Ɗorayi Chiranchi ana zarginsa da  kashe wani matashi mai suna, Zahraddeen Iliyasu ta hanyar caka masa wuƙa a wuya bayan da suka samu saɓani.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Ya ce an kama matashin ne lokacin da yake ƙoƙarin tserewa ya zuwa ƙasar Jamhuriyar Nijar.

More from this stream

Recomended