Ƴan majalisa a Najeriya na neman ƙarin albashi

‘Yan majalisar wakilai na neman a sake duba albashinsu da alawus-alawus, biyo bayan cire tallafin man fetur da kuma halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a halin yanzu.

Rahotanni sun nuna cewa an nuna bukatar hakan ne a taron da ‘yan majalisar suka yi a ranar 11 ga watan Yuli bayan sun shiga zaman zartarwa a zaman majalisar.

‘Yan majalisar sun kuma bukaci shugaban majalisar, Tajudeen Abass, dalilin da ya sa aka jinkirta biyansu albashi da alawus-alawus, lamarin da ya sa wasu daga cikinsu ke neman lamuni.

Sai dai daya daga cikin ‘yan majalisar da ya halarci taron amma ya bukaci a sakaya sunansa saboda ba a ba shi damar yin magana kan sakamakon zaman majalisar zartarwa ba, ya ce sun yi maganar karin albashi ne kawai ba tare da jinkiri ba.

More from this stream

Recomended