Ƴan kudu sun tunzura ƴan arewacin Najeriya kan matsalar tsaronsu

..

Ƴan Najeriya musamman ƴan arewacin ƙasar sun jima suna ta kiraye-kiraye kan soke rundunar da ke yaƙi da fashi da makami ta SARS.

Sun kuma sha yin zanga-zangar lumana kan tituna, a wani lokacin kuma a kafafen sada zumunta inda suke amfani da mau’du’in #ENDSARS.

Suna gudanar da zanga-zangar ne sakamakon zargin da suke yi wa rundunar ta SARS da azabtarwa da kisa ba bisa ƙa’ida ba da kuma saɓa ƙa’idojin aiki.

Sai dai a wannan karon, da alamu haƙarsu ta soma cimma ruwa sakamakon dagewa da suka yi kan wannan zanga-zanga, lamarin da har ya ja hankalin shugaban ƙasar ya fito ya ce zai ɗauki matakin kawo sauyi a rundunar.

Shugaban ya ce ana kawo masa bayanai lokaci bayan lokaci kan sauyin da ake yi domin kawo ƙarshen azabtarwar da ‘yan sandan ke yi.

Ganin yadda musamman ‘yan kudancin ƙasar suka dage da mau’du’in #ENDSARS kuma har ya ja hankali a cikin gida da waje, hakan ya tunzura wasu ‘yan arewacin Najeriyar suka fara amayar da abin da ke cikinsu dangane da halin da yankin ke ciki na rashin tsaro.

A yanzu dai, mau’du’in #EndSarsNow ya haifar da mau’du’in #EndNorthBanditry wanda akasari ‘yan arewacin Najeriyar ne ke kira ga gwamnatin ƙasar ta kawo ƙarshen ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro da ke addabar yankin.

Me masu neman kawo ƙarshen rundunar SARS ke cewa?

Ɗumbin jama’a ne ke ci gaba da zanga-zanga a jihohin Najeriya da dama da suka haɗa da Legas da Kaduna da Oyo da birnin Abuja.

Ko a ranar Juma’a sai da masu zanga-zangar suka yi zaman dirshen a gaban gidan gwamnan Legas inda suka kwana a wurin.

Haka ma a Abuja da Legas ɗin sai da ‘yan sanda suka tarwatsa wasu daga cikin masu zanga-zangar da hayaƙi mai sa hawaye.

Ga dai abin da wasunsu ke cewa:

Olorunshola Emmanuel a shafin Twitter ya bayyana cewa a yanzu haka suna gaban hedikwatar ‘yan sanda ta Abuja. A cewarsa, abin da suke nema kawai shi ne a daina kashe su, matasan Najeriya na da damar rayuwa cikin walwala.

Wannan kuma cewa ya yi masu zanga-zanga a Abuja abu ɗaya kawai suke nema, wato babban sifeton ‘yan sandan ƙasar ya yi musu jawabi.

Wannan kuma cewa ya yi ba su son a sauya yanayin tsarin rundunar SARS, so suke yi a kawo ƙarshenta.

Yadda mau’du’in #EndSarsNow ya haifar da mau’du’in #EndNorthBanditry

Wannan kuma yana kira ne ga ‘yan arewacin ƙasar da su ninka kiraye-kirayen da suke na kawo ƙarshen rashin tsaro a arewacin ƙasar, inda yake jan hankalinsu da su dubi yadda jama’ar kudancin ƙasar ke amfani da ƙarfinsu wurin zanga-zanga domin jan hankalin gwamnatin ƙasar.

Wannan cewa ya yi “Rundunar SARS na kashe ‘yan kudu, ɓarayi da ‘yan Boko Haram na kashe ‘yan arewa, muna buƙatar gwamnatin tarayya ta kawo ƙarshen rundunar SARS da kuma satar da ake yi a arewa, ana zubar da jini a Najeriya, ya kamata gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa kan abubuwan da ke faruwa.

Ita ma fitacciyar jaruman fina-fanan Kannywood Rahma Sadau ba a bar ta a baya ba inda ta ce a shirye take ta ɗaga muryarta wurin kawo ƙarshen rashin tsaro da ke faruwa a arewacin Najeriya.

Me gwamnatin ƙasar ke cewa?

Da dama daga cikin masu mulki a ƙasar na bisa ra’ayin cewa ba su amince da a soke rundunar SARS ba, sai dai a yi mata sauyin fasali.

A saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, ya ce ba ya goyon bayan soke rundunar sakamakon soke ma’aikatu irin haka ba shi ba ne abin da ya dace.

A saƙon da ya wallafa shi ma a shafinsa na Twitter, Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila shi ma ya fi karkata ne kan kawo sauyi ba wai rushe rundunar baki ɗaya ba.

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan kafofin sada zumunta Lauretta Onochie, ta bayyana ra’ayinta a shafin Twitter inda ta ce ba za a iya soke rundunar SARS ba, a cewarta, ya kamata a rinƙa hukunta ‘yan sandan da suka saɓa doka, haka ne kawai hanyar da za a bi a kawo sauyi, in ji ta.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...