Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Wani Fitaccen Ɗan Kasuwa Tare Da Yin Garkuwa Da Ƴarsa Da Matarsa A Jihar Katsina

Ƴan fashin daji  sun kai farmaki ƙauyen Mairuwa dake ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina ranar Asabar da daddare dai-dai lokacin da ake gudanar da Sallar Tarawih.

A kalla mutane biyu aka harbe s har lahira a yayin da mutum guda kuma ya jikkata.

Ɗaya daga cikin mutanen da aka kashe, Alhaji Lado fitaccen ɗan siyasa ne kuma babban manomi ne a garin.

Wata majiya dake garin ta ce an kashe marigayin ne bayan da ya nuna turjiya lokacin da ƴan fashin dajin suke ƙoƙarin tafiya da shi.

Wani mutum da ya tsira daga harin ya ce ƴan bindigar sun samu nasarar yin garkuwa da mata da kuma biyu daga cikin ƴaƴan marigayin.

Mutum na biyu da aka kashe a harin wani ma’aikacin lafiya ne da yake aiki a Cibiyar Kula Da Lafiya ta Mairuwa.

More from this stream

Recomended