Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban jami’a 20 a Benue

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu ɗaliban aikin likita su 20 a jihar Benue.

Ɗaliban da aka sace sun fito ne daga jami’ar Maiduguri da kuma jami’ar Jos a yayin da ƴan bindiga suka yi musu harin kwanton ɓauna a yankin  Otukpo dake jihar Benue da maraicen ranar Alhamis.

Suna kan hanyarsu ne ta zuwa Enugu domin halartar taron shekara na ƙungiyar ɗaliban aikin likita da na likitan hakori mabiya cocin katolika da za a gudanar a jihar ta Enugu.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Benue, Catherine Anene ta tabbatarwa da  jaridar The Cable faruwar lamarin.

“Ɗaliban sunzo wucewa ne ta cikin jihar Benue zuwa Enugu lokacin  da aka yi awon gaba da su. Yanzu haka ana cigaba da gudanar da bincike,” ta ce.

A ƴan kwanakin nan dai ana cigaba da samun ƙaruwar yawan masu garkuwa da mutane a sassa daban-daban na Najeriya.

More from this stream

Recomended