
Yakubu Lawal, kwamishinan yada labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar Nasarawa wanda yan bindiga suka yi garkuwa da shi ya shaki iskar yanci.
Ramhan Nansel, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Nasarawa, shi ne ya sanarwa da kamfamin dillancin labarai na Najeriya NAN haka ranar Juma’a.
Kwamishinan an yi garkuwa da shi a ranar Litinin a gidansa dake Nasarawa Eggon.
Nansel ya ce kwamishinan ya shaki iskar yanci da misalin karfe 06:00 na yammacin ranar Juma’a kuma tuni ya isa gida wurin iyalinsa.
Mai magana da yawun rundinar ya ce babu wani da aka kama da zargin sace shi.