Ƴan bindiga sun sace wa da ƙane a Zariya

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da yin garkuwa da wani ma’aikacin lafiya tare da dan uwansa a daren Juma’a a unguwar Wusasa da ke karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna.

‘Yan bindigar sun kai farmaki yankin ne da misalin karfe 9 na dare inda suka yi ta harbe-harbe don tarwatsa jama’a kafin su dauko wadanda suka kama, Yushau Peter na Asibitin St. Luke Wusasa da dan uwansa, Joshua Peter.

Hakimin kauyen Wusasa Injiniya Isiyaku Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya koka da cewa, “Masu garkuwa da mutane sun sha mayar da yankinmu inda suke kai hare-hare, tare da yin garkuwa da da dama daga cikin mutanenmu.

Ya kara da cewa a unguwar Wusasa da ke wajen tsohon birnin Zazzau, an sha fama da hare-hare a ‘yan kwanakin nan, inda ya ce ba da dadewa ba ne aka kashe wani jami’in soji da dan banga.

More from this stream

Recomended