Ƴan bindiga sun kashe sarakuna biyu a jihar Ekiti

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe sarakuna biyu a jihar Ekiti a ranar Litinin.

Sarakunan biyu na kan hanyarsu ne ta dawowa daga wani taro da suka halarta a Irele-Ekiti inda aka biyo sawunsu aka bindige su har lahira.

Oba David Ogunsakin, mai rike da sarautar Elesun na Esun-Ekiti; da kuma Oba Olatunde Olusola, mai rike da sauratar Onimojo na Omojola-Ekiti sune sarakunan da aka kashe.

Sunday Abutu mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya tabbatar kisan sarakunan biyu.

Abutu ya kara da cewa tuni aka tura tawagar jami’in sirri na rundunar ya zuwa yankin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa Oba Adebayo Fatoba, Alara na Ara-Ekiti ya tsira da ransa a harin.

Da yake mayar da martani kan faruwar lamarin gwamnan jihar Ekiti Biodun Oyebanji ya umarci rundunar ƴan sandan jihar su zakulo wadanda suka aikata laifin.

More from this stream

Recomended