Ƴan bindiga sun kashe jami’in NDLEA tare da yin garkuwa da mutane 3 a Sokoto

Wasu ƴan bindiga da ba’asan ko suwaye ba sun harbe wani jami’in hukumar NDLEA dake hana sha da kuma fataucin miyagun ƙwayoyi kana suka kuma yi garkuwa da wasu mutane 3 akan titin zuwa filin jirgin saman Sultan Abubakar dake Sokoto.

Wani mazaunin yankin da abun ya faru, Muhammad Baba Usman wanda ɗansa na daga cikin waɗanda aka sace ya ce ƴan bindigar sun kai harin ne da misalin ƙarfe 09:30 na dare.

“Su huɗu ne dukkaninsu ɗauke da bindiga. Sun zo a cikin mota da suka ajiye ta a bakin titi.Dukkansu sun fito suka fara harbin kan me uwa da wabi mutum guda harsashi ya sama ya kuma mutu akan hanyar zuwa asibiti,”

“Sun kuma yi awon gaba da mutane uku ciki har ɗa na. Har yanzu muna jiran kiran wayarsu muji abun da za su buƙata.” A cewar Muhammad

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmed Rufa’i ya tabbatar da cewa wanda ya mutu ma’aikci ne a hukumar NDLEA.

A cewar Rufa’i ƴan sanda na bin sawun masu garkuwa da mutanen.

More News

Mutane 11 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutanen da basu gaza 11 ne ba aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 16 suka jikkata mutum ɗaya kuma ya tsira...

Ƙasar Amurika ta fara shirin kwashe sojojinta daga Nijar

Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CBS ta bada rahoto. Wani jami'in ma'aikatar wajen...

Sojoji sun kashe ƴan ta’adda biyu tare da gano makamai a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu ƴan ta'adda biyu a ƙauyen Kana dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno. A wata sanarwa ranar Asabar...

An halaka mutane 6 a wani faɗa tsakanin ƴanbindiga da ƴanbanga

Mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga da aka fi sani da ‘Yan...