Ƴan bindiga sun kai farmaki kan rukunin wasu jami’an ƴan sanda dake aikin sintiri a Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi inda suka kashe huɗu daga ciki .
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe biyar na ranar Juma’a a wurin shingen binciken ababen hawa na gadar Ebyia dake kan titin Hill Top a Abakaliki.
An kuma kashe fararen hula biyu a lokacin da ake musayar wuta tsakanin ƴan sandan da kuma yan bindigar.
Joshua Ukandu mai riƙon muƙamin kakakin rundunar yan sandan jihar ya ce ana zargin cewa ƴan bindigar mambobi ne na ƙungiyar IPOB dake fafutukar samar da ƙasar Biafra.
“Ƴan sandan sun yi musayar wuta sosai da ƴan bindigar a musayar wutar ne ɓatagarin suka gudu har suka bar bindiga guda ɗaya,” Ukandu ya ce.
Ya ƙara da cewa ƴan sanda na cigaba da bibiyar ƴan bindigar.