
Ƴan wasa da kuma jagororin kungiya ne suka jikkata a wani hari da ƴan bindiga suka kai kan tawagar kungiyar kwallon kafa ta Sunshine Stars dake Akure.
Ƴan bindigar sun bude wuta ne kan motar kungiyar kwallon kafar akan hanyar Benin-Ore.
Acikin wata sanarwa, Michael Akintunde jami’in hulɗa da jama’a na kungiyar ya ce an kai harin ne da maraicen ranar Alhamis.
Ya ce tawagar ƴan wasan na kan hanyar zuwa Benin ne domin buga wasan mako na 13 na gasar kungiyoyin kafa ajin kwararru ta NPFL da kungiyar Bendel Insurance dake Benin.
Akintunde ya ce babu wanda ya rasa ransa a harin sai waɗanda suka jikkata.