Ƴan bindiga sun kai farmaki hedkwatar ƙaramar hukumar, Isiala Mbano dake jihar Imo da tsakar daren ranar 3 ga watan Satumba inda suka ƙone gine-gine da dama tare da kashe jami’an tsaro.
Maharan sun kai farmakin ne da misalin ƙarfe 08:30 zuwa 09:30 na dare sun kuma gaggauta tserewa daga wurin.
An kai hari ne dai-dai lokacin da ake gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyar APC domin zaɓen yan takarar shugabannin ƙananan hukumomi da na kansiloli na ƙananan hukumomin jihar 27 da mazaɓu 305.
A cewar rahotanni cikin waɗanda aka kashe akwai ƴan kungiyar Ebubeagu ta samar da tsaro a yankin kudu maso gabas da gwamnati ta kafa. Kawo yanzu babu wata kungiya da ta ɗauki nauyin alhakin harin kuma rundunar ƴan sanda bata fitar da wata sanarwa ba kan harin.
A wani lamari mai kama da haka wasu maharan sun kai irin wannan hari hedkwatar ƙaramar hukumar Otoko dake shiyar Okigwe a jihar.
Kwamshinan ƴan sanda na jihar, Aboki Danjuma ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce rundunar da haɗin gwiwa sauran hukumomin tsaro na yin bakin ƙoƙarinsu domin mayar da martani kan harin da ake zargin ƴan kungiyar IPOB dake fafutukar kafa ƙasar Biafara da karawa.