Ƙungiyar Izala: Shin gwamnatin Najeriya za ta ba da bashi ta hannun ƙungiyar?

  • Umar Mikail
  • BBC Abuja Bureau
Bayanan hoto,
Saƙon da aka yaɗa a WhatsApp bai bayyana adadin kuɗin da za a bai wa mutane ba a matsayin bashin

Wani saƙo da ake yaɗawa ta dandalin WhatsApp ya buƙaci mutane su yi rajistar neman bashin kuɗi daga Gwamnatin Tarayyar Najeriya.

Saƙon ya yi ikirarin cewa za a bayar da bashin ne ta hanyar ƙungiyar addinin Musulunci ta Izala tare da sahalewar Shiekh Dakta Bashir Aliyu Umar, Babban Limamin Masallacin Al-Furqan da ke Jihar Kano.

Kamar yadda aka rubuta a saƙon: “Ku yi kokari kuyi apply loan ne da gwamnatin najeriya zata bayar karkashin kuniyar IZALA. Sannan ku turawa yan uwa musulmai link din www.manaraabp.com.”

Saƙon ya ci gaba da cewa: “Wannan shine kadai ingantaccen Link din saboda haka idan aka samu wani sabanin wannan to kada ayi amfani dashi. kuma ya samu sahalewa ne daga Babban Malami DR. BASHIR ALIYU UMAR (ALFURQAN).”

Mene ne gaskiyar ikirarin?

Tuni shehin malami Dakta Bashir Aliyu ya musanta cewa wannan bayani daga wurinsa ya fito.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shaifinsa na Facebook, malamin ya ce duk wata sanarwa daga wurinsa za a same ta ne kawai ta sahihiyar kafa ko kuma wannan shafin nasa na Facebook .

“Ƴan uwa Musulmi wannan rubutu mai haɗe da link http://www.manaraabp.com a kan bashi na Manara ba ni da alaƙa da shi, don haka a guji yaɗa duk wata jita-jita mai alaƙa da wannan da sunana,” in ji Dakta Bashir.

Farfesa Salisu Shehu na Jami’ar Bayero ta Kano ya wallafa hotunan wani taron wayar da kai da suka gudanar a Kano game da yadda za a nemi bashin Babban Bankin Najeriya CBN maras ruwa.

Abin da ya kamata a lura da shi

Binciken da BBC ta gudanar ya gano cewa wannan saƙo da ake yaɗawa ba na gaskiya ba ne, wasu ne ke yaɗa shi domin cimma wata buƙatarsu ta musamman.

Idan aka lura da saƙon, za a fahimci cewa akwai kura-kurai da yawa game da yadda aka rubuta shi – an karya ƙa’idojin rubutu masu yawa a ciki, hakan na nuna cewa ba masu ilimi ne sosai suka rubuta shi ba.

Shi kansa shafin http://www.manaraabp.com da aka ce ta nan ne za a nemi bashin, ba ya aiki yadda ya kamata. Misali babu bayanan masu shafin da za ku iya tuntuɓarsu idan kuna neman ƙarin bayani.

Kazalika form ɗin da za a cike ɗin bai bayar da damar saka wasu muhimman bayanai ba game da muradin da mutum yake so ya cimma idan an ba shi bashin, wanda dole ne a yi bayani idan har bashin sahihi ne.

Kazalika babu gurbin da mutum zai cike adadin kuɗin da zai iya nema, abin da ya saɓa da abin da aka saba gani.

Hasali ma sun fi ƙarfafa neman bayanan mutum na sirri irinsu lambar BVN ɗin mutum da ta matarsa ko mijinta da kuma ta magajinsa wato next of kin – lambar BVN uku kenan suke nema.

Hakan yana nuna cewa sun fi damuwa ne da su samu bayanan fiye da buƙatar wanda ya je neman bashin, kuma za a iya amfani da bayanan domin a zambaci masu su.

Sabon salon yaɗa labaran ƙarya

Masu yaɗa labaran ƙarya sun daɗe da wayewa tare da sauya salon ci gaba da mamugunciyar sana’ar tasu.

Yanzu sun daina ƙirƙirar wani abu sabo fil wanda babu shi su ce ya faru.

Akasari suna fakewa ne da wani abu da ya yi kama da gaskiya ko kuma gaskiyar ce amma sai a sauya mata fuska.

Misali, da gaske ne cewa gwamnatin Najeriya na bayar da bashi, waɗannan sun yi amfani da gaskiyar ce domin neman bayanan mutane ta wani shafi daban ba ainihin na gwamnatin ba.

Yadda ake gane labaran karya

Akwai yiwuwar ci gaba da samun labaran karya, musamman a lokutan zabuka.

Kamfanonin sada zumunta kamar Twitter da Facebook sun bayyana shirinsu na yakar sana’ar yada labaran karya a duk fadin duniya, amma ga wasu hanyoyi biyar da za ka iya kawar da yada bayanan da ba su da tushe:

Bayanan hoto,
Mutane da dama aka kashe a rikicin manoma da makiyaya wanda aka ce labaran karya na kara zuzutawa

Mutane da dama aka kashe a rikicin manoma da makiyaya wanda aka ce labaran karya na kara zuzutawa

Shafukan sada zumunta na karya kan yi kokarin bayyana kansu a matsayin cewa sun fito ne daga manyan kafofin watsa labarai, a don haka ka duba shafi sosai kafin ka watsa bayanan da suka wallafa.

Shafukan da aka tabbatar da halaccinsu suna dauke da alamar shudi a Facebook, da Twitter da kuma Instagram.

Duk da cewa wannan wani lokaci ba zai gamsar ba amma yana da kyau a duba abin da wasu kafofin watsa labarai masu inganci ke cewa kan labari domin tabbatar da gaskiyar batu.

Tambayi kanka, shin ingantattun kafafan yada labarai na bada rahoton wannan labarin?

Akwai hanyoyi da dama da za su taimaka maka wurin tabbatar da sahihancin hoto ko bidiyo. Google, da Bing da kuma Tin Eye duk suna duba asalin hoto, wanda kan iya gaya maka inda aka dauki hoto da kuma asalinsa.

Tabbatar da bidiyo ya fi wahala amma shafuka kamar InVid na bada damar gano inda aka yi amfani da bidiyon da aka wallafa a Facebook da YouTube a baya.

Idan kana da ainahin hoton ko bidiyo, za ka iya samun bayanai masu muhimmanci game da su, ciki har da wuri da kuma lokacin da aka dauka da kuma na’urar da aka yi amfani da ita.

Abin takaicin shi ne da zarar an wallafa hotuna a shafukan sada zumunta to bayanansu na sali sai su bace.

Yi tunani kafin ka wallafa

Dole a yi taka-tsan-tsan saboda ka da a kara jefa mutane cikin rudani.

Kafin ka wallafa, ka tambayi kanka ko bayanan da ka ke da su sun inganta kuma ya karfin sahihancinsu yake.

More News

Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma'aikata 6 ya gamu da matsala...

Ɗan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...