Zulum ya gana da Tinubu, ya ce babu wata karamar hukuma da za ta sake koma karkashin yan ta’adda

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ce babu wata karamar hukuma a jihar Borno da za a bari ta fada karkashin ikon yan ta’adda.

Zulum ya fadi haka ne a ranar Litinin lokacin da ya ke magana da yan jaridu jim kadan bayan ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Gwamnan ya ce ya gana da shugaban kasar domin sanar da shi kalubalen tsaro tsda ake fama da shi a jihar Borno da kuma sauran sassan arewacin Najeriya.

“Abubuwa basa tafiya dai-dai a arewacin Najeriya musamman ma a yankin arewa maso gabas,” ya ce.

Zulum ya ce a yan kwanakin nan yan ta’adda sun zafafa kai hare-hare a jihar kan sansanin sojoji da kuma jama’ar gari.

Ya ce gwamnatin tarayya tana amsa rokon jihar na kawo dauki.

Ya lura da cewa yan ta’addar na cigaba da amfani da makamai na zamani a hare-haren da su ke kai wa.

Ya ci alwashin cewa babu wani bangare na jihar da zai fada karkashin yan ta’adda.

Ya kara da cewa “Ba zai taba faruwa ba yanzu. Na yarda Insha Allah da taimakon rundunar sojan Najeriya baza mu bari karamar hukuma daya ta koma karkashin yan ta’adda na,”

Zulum ya bayyana kwarin gwiwar cewa kokarin da ake tsakanin gwamnatin tarayya da ta jiha zai haifar da sakamako mai kyau.

More from this stream

Recomended