Zargin Batanci: An Yi Ajalin Wata Mata A Jihar Neja

Wata mata mai suna Amaye ta rasa rayuwarta a garin Kasuwan-Garba da ke Karamar Hukumar Mariga, Jihar Neja, bayan wasu matasa sun yi mata duka tare da kona ta, bisa zargin ta yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Lamarin ya faru ne a daren Asabar, inda ake cewa marigayiyar, wadda ke da wajen sayar da abinci, ta yi maganganun da aka dauka a matsayin batanci a wajen cin abinci nata.

Rahotanni sun bayyana cewa wani kwastoma ya yi mata barkwanci da cewa yana son ya aure ta, yana danganta maganarsa da al’adun Annabi, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Wata majiya ta shaida cewa daga bisani al’ummar yankin sun kai matar fadar Sarkin Kasuwan-Garba, inda daga nan aka mika ta ga jami’an tsaro domin gudanar da bincike. Sai dai kafin a kai ga daukar matakin tsaro mai inganci, matasan gari sun mamaye jami’an tsaron, suka kashe ta sannan suka banka mata wuta.

Shugaban karamar hukumar Mariga, Abbas Adamu Kasuwan-Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa an dawo da zaman lafiya a yankin.

More from this stream

Recomended