Zanga-zanga: An jibge ƴan sanda 4200 a Abuja

Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta tura ƴan sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta.

Kamar yadda masu shirya zanga-zangar suka faɗa za a fara jerin gwano na tsawon kwanaki 10 daga ranar 1 ga watan Agusta.

A wata sanarwa ranar Juma’a, Josephine Adeh mai magana da yawun rundunar yan sandan birnin ta ce an jibge jami’an tsaron ne domin tsaron lafiyar jama’a, ta masu zanga-zanga da kuma hana ɓata gari shiga zanga-zangar.

Adeh ta ce Benneth Igweh kwamishinan ƴan sandan  birnin ya tabbatarwa da mazauna birnin cewa jami’ansa za su kare rayuka da dukiya baza kuma su lamunci aikata ɓarna ba.

Ta shawarci mazauna birnin da su kai rahoton duk wani motsi da basu yarda da shi ba.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...